top of page
Search

UNTITLED

  • duelpoetic
  • Jul 28, 2021
  • 1 min read

Rayuwar ga da aka ƙayyade mini

Yau na riski wa'adi ba mai hana mini

Zan amsa kirar da jalla yai mini

Fata na da roƙo can ya fiye mini.


Babu dabara ta likita ko jiƙo

Zan bar duniyar ga mai amo

Na sarewa, algaita da liƙo

Tarihi a yau, tabbas zan zamo.


Ina ƙira ga 'yan uwa da abokai ga ni

Kuka kada kui sam ga ni

Du'a'i nake so kui mini

Ga jalla mamallakin dukkan zamani.



HABAR

 
 
 

Comentarios


Post: Blog2_Post

Subscribe Form

Thanks for submitting!

+2348146351050

  • Facebook
  • Twitter
  • LinkedIn

©2020 by poetic duel. Proudly created with Wix.com

bottom of page